Hakan na zuwa ne da nufin nuna rashin jin dadinsu game da jan kafar da ake fuskanta wajen soma zartar da matakin sassauta harajin kayan abinci kamar yadda fra ministan kasar ya yi alkawali a yayin wata ganawa da shugabannin ‘yan kasuwa a ranar 19 ga watan maris inda aka tantauna hanyoyin magance matsalolin dake haddasa tsadar ababen masarufi.
Firai minista Ouhoumoudou Mahamadou ya yi yi wa shugabannin ‘yan kasuwa albishir a game da matakan da gwamnatin Nijer ta dauka da nufin shafe masu hawaye sakamakon tarin matsalolin da suke dauka a matsayin dalilan hauhawar farashin kayan abinci a wani lokacin da al’umar musulmi ke shirin fara azumin Ramadan.
Ya kara da cewa, gwamnatinsa ta tuntubi hukumomin Jamhuriyar Benin domin bai wa jiragen dakon kaya izinin safke kayan ‘yan kasuwar Nijer dake jibge a tsahar jirgin ruwan Cotonou.
Sannan ya umurci ma’aikatar kudin kasa da ta haraji da su sassauta kudaden wani harajin da ‘yan kasuwa ke biya a can baya haka kuma aka dauki matakin takaita yawan shimgayen bincike akan hanyoyin zirga zirga ba ya ga wasu muhimman matakan da aka dauka akan wasu matsalolin da ‘yan kasuwa suka koka akansu inda a karshe aka dora nauyin zartar da wadanan matakai a wuyan wani kwamitin hadin guiwa.
Sai dai kwanaki 10 bayan haka har yanzu ba wani sauyin da aka samu a aikace inji shugaban kungiyar ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga waje Alhaji Sani Chekarao.
Sabon tsarin biyan kudaden harajin TVA ta hanyar amfani da na’ura wato facture certifiee na daga cikin abubuwan da gwamnatin tace ta dauki matakin sassauci a kansu to amma a cewar kungiyoyin ‘yan kasuwa soke wannan tsari itace hanya mafi a’ala a gare su saboda haka ne suka yi barazanar rufe kasuwanni a ranar alhamis din dake tafe.
Wannan shi ne karo na 2 da ‘yan kasuwar Nijer ke shiga yajin aiki akan wadanan matsaloli masu nasaba da biyan diyyoyin kasa saboda a cewarsu tarnaki ga ci gaban harakokin kasuwanci a wani lokacin da duniya ke fama da kalubale da dama cikinsu har da matsalolin tsaro da illolin canjin yanayi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
'