Nijar Na Fatan Taron Kasashen Afirka Da Rasha Ya Amfani Talakawa

Taron Shuwagabannin Kasashen Afrika A Kasar Rasha

Shugabanin kasashen Afirka na ci gaba da tattaunawa da hukumomin kasar Rasha, wuni na biyu na taron da suke gudanarwa a birnin Sotchi, da nufin karfafa hulda a fannoni da dama. Wadanda suka hada da sha’anin ma’adanai, kasuwanci, noma, kiwo, da kuma matsalar tsaro da ta addabi galibin kasashen nahiyar ta Afirka.

A ra’ayin ministan watsa labaran jamhuriyar Nijar, Salissou Mahaman Habi, wannan wata dama ce da Afirka ta samu don gwadawa duniya cewa sun waye.

Lura da yadda manyan kasashen Yammacin Duniya, da wasu takwarorinsu na nahiyar Asia, suka yiwa nahiyar Afirka ca akai, yasa ta hanyar diflomasiyya, kasar Rasha sake jan damara da nufin kyautata dadaddiyar dangantakarta da kasashen Afirka, dalilin wannan taro na birnin Sotchi.

Batun tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da kasashen Afirka ke da damuwa akai, musamman ta’addancin da ya addabi Yankin Sahel. Saboda haka ake ganin taron na iya zama wata damar tattauna hanyoyin hada makaman yaki a wajen wasu kasashen.

Ga cikakken rahoto daga wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwmnatin Nijar Na Fatan Taron Afirka Da Russia Zai Amfani Talakawa