Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta ba da tabbacin cewa kayayyin zabe za su isa rumfuna zaben akan kari da sassa dabdan daban na kasar.
WASHINGTON D.C. —
Mataimakiyar shugaban hukumar Hajiya Maryama Katambe ce ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma.
Ta ba da tabbacin cewa komai na tafiya daidai yayin da ake shirin gudanar da zabukan a gobe Lahadi.
Zabukan da za a yi sun hada da na shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisu, zaben da gwamnati mai ci ta ke ikrarin za ta lashe tun a zagayen farko yayin da su ma ‘yan adawa ke cewa su za su samu nasara a zagayen na farko.
Saurari cikakkiyar hirar Hajiya Maryama Katambe da wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5