Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Nijar mazauna kasar Kamaru na shirin yin zabe a kananan ofisoshin jakadancinsu


Wasu cikin wuraren da 'yan Nijar zasu jefa kuri'u
Wasu cikin wuraren da 'yan Nijar zasu jefa kuri'u

Yayinda saura kimanin kwana uku a fara zaben shugaban kasar Nijar da na 'yan majalisu, 'yan kasar dake Kamuru a shirye suke su kada tasu kuri'un a zaben ranar 21 ga watan Fabrairu.

Kqwanaki uku ya rage a gudanar zaben a kasar jamhuriyar Nijar haka ma lamarin yake a jamhuryar Kamaru inda 'yan asalin kasar Nijar ke zuwa kananan ofishin jakadanci suna bukatar takardunsu domin su jefa tasu kuri;un.

Shi dai zaben na kasar Nijar za'a yi shi ne ranar Lahadi 21 ga wannan watan. Alhaji Audi shugaban jam'iyyar LUMANA a kasar Kamaru ya kira jama'a su karbi takardun jefa kuri'a saboda zabe ba zai yiwu ba saida takardun zabe.

Wani Zakari Haruna shi ne jagoran kungiyar da ta je Kamaru domin raba katuna. Sun shirya kowa zai yi zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba. Ya bayyana inda za'a yi zaben domin kowa ya sani.

Dangane da samun tsaro Zakari Haruna yace sun nemi kariyar jama'ain tsaro kuma zasu kasance wurin zaben.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:15 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG