NIJAR: Manyan 'Yan Jam'iyar RDR Canji Sun Canza Sheka

Taron Jami'yyu a nijar

Fitaccen dan siyasa a Jamhuriyar Nijar Doudou Rahama na hannun daman tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman da magoya bayansa ,sun bada sanarwar canza sheka daga jam’iyar RDR Canji zuwa PNDS Tarayya ta shugaba Mohamed Bazoum.

Bisa ga cewarsu, sun tsaida shawarar ficewa daga jam’iyar ne bisa zargin uwar jam’iyar ta RDR Canji da kaucewa manufofin jam’iya na ainahi , sai dai wasu magoya bayan shugaba Ousman na cewa ‘’ko a ka’’.

Doudou Mahamadou wanda aka fi sani da Doudou Rahama na daya daga cikin manyan ‘yan gani-kashenin tsohon shugaban kasar Nijer Mahaman Ousman tun a zamanin jam’iyar CDS Rahama kafin rikicin shugabanci ya tilasta masu komawa jam’iyar MNRD Hakuri, sannan daga bisani suka kafa jam’iyar RDR Canji wace a karkashinta Mahaman Ousman ya shiga zaben shugaban kasa na 2020. Sai dai tun a washegarin zaben da aka bayyana shugaba Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara dangantaka ta fara tsami a tsakanin Ousman da Doudou Rahama mafarin ficewarsa daga wannan jam’iya saboda dalilai na rashin fahimtar juna.

Da yake jawabi bayan sanar da sake shekarar ‘yan siyasan. Issa Maman Galadima, shugaban matasan Canji.

Alhaji Doudou Rahama wanda tun fil azal ke matsayin kakakin Mahaman Ousman wanda ya rike irin wannan mukami a tsawon fshekaru fiye da 10 na mulkin PNDS a matsayin mai magana da yawun kwancen jam’iyun hamayya. Kakakin PNDS Tarayya na kasa Assoumana Mahamadou ya bayyana farin cikin zuwan mutunen da ya kira dadadun abokan gwagwarmaya.

A karshen makon nan ne sabon dan Tarayya Doudou Rahama da magoya bayansa za su gudanar da taron gangami domin jaddada matsayinsu game da sabuwar tafiyar siyasar da suka runguma wace wasu bayanai ke cewa akwai kansiloli da magaddan gari har ma da ‘yan majalissar dokokin kasa da suka yi na’am da ita.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

CANZA SHEKAR GAGGAN YAN JAM IYAR RDR CANJI.MP3