Kiristan za su yi hakan ne don nuna murnar ranar tashin mutumin da su ka yi imani ya zo duniya ne domin ceton al’ummomi daga zunubi.
Mahimmancin Ista a wajen mabiya addinin krista ya sa majami’u ke cikar da ba kasafai ake ganin irinta ba, sai a irin wannan lokaci na nuna farin cikin tashin annabi Isa bayan mutuwar kwanaki 3, taron wanda a yayinsa krista kan yi sujjada a ranar Lahadi lokaci ne na lillika addu’oi. Malama Elisabeth Zakari Barao da ke jihar Tahoua na daga cikin masu zumudin zuwan wannan rana.
Krista kan gayyaci danginsu da abokan zama albarkacin wannan salla domin karfafa dankon zumunci ba tare da la’akari da bambancin addini ba. Malan Yahaya Nomao ya yaba da irin wannan halayya.
Da yake ‘yan magana na cewa salla wasan daya rana, uwaye mata na gargadin takwarorinsu da su yi aiki da dan abinda ya sauwaka a yayin wannan buki.
A jiya juma’ar da ake yi wa lakabin Good Friday kokuma Vendredi Saint a Faransance a nan Nijer krista sun cika dare suna addu’o'i kamar yadda aka saba idan ranar dake daidai da mutuwar Annabi Isa ta zagayo, sun kuma yi amfani da wannan dama domin yi wa kasa da makwaftanta addu’o'in neman mafitar matsalolin tsaron da ake fama da su a ‘yan shekarun nan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5