An yi hakan ne da nufin tantance abubuwan dake bukatar gyara musamman dai wadanda suka shafi bukatun talakawa kafin zuwan ranar da ‘yan majalisar zasu yi kuri’a akan wannan kasafi mai kunshe da biliyon sama da 2000 na kudaden CFA.
Da irin wadanan bayanai na masana a sha’anin tattalin arziki aka fara zaman bajewa wakilan kungiyoyin fararen hula mahimman gabobin da kasafin kudaden 2022 ya kunsa.
Kungiyar Alternative Esapce Citoyen da hadin guiwar kungiyar ROTAB Niger ne suka shirya wannan taro a matsayin wata hanyar fahimtar da jama’ar wannan kasa tanade tanaden da gwamnati ta yi a matsayin abubuwan da take fatan aiwatarwa a badi yayinda a daya gefe abin ke zama wata hanyar jan hankulan ‘yan majalisa a game da abubuwan dake bukatar dubawa kafin su amince da kudirorin na bangaren zartarwa.
Gomman wakilan kungiyoyi daga sassan kasa ne ke halartar wannan taro na shekara shekara wanda ke zama wata damar tantance ainahin kason da aka ware wa fannoni daban daban.
A karshen wannan taro na tsawon kwanaki 3 da ake kira Session Budgetaire kungiyar AEC da ROTAB Nijer zasu tattara shawarwarin da aka tsayar domin gabatar da su ga majalisar dokokin kasa wacce ke da wuka da nama wajen tabbatar da kasafin na sabuwar shekara ko sake mayar da shi bangaren zartarwa domin gyara.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5