Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kara Kason Kudaden Tafiyar Da Ilimi A Kasafin Kudinta


Buhari yarin da yeke gabatar da wata takarda gabanin taron kolin da za a yi a London kan ilimi (Facebook/Femi Adesina)
Buhari yarin da yeke gabatar da wata takarda gabanin taron kolin da za a yi a London kan ilimi (Facebook/Femi Adesina)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar da kara kashi 50 cikin 100 a kasafin kudin tafiyar da bangaren ilimi a kasar a cikin shekaru biyu masu zuwa, da kuma kashi 100 a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron karawa juna sani kan ilimi na duniya mai taken "daukar nauyin hadin gwiwa a bangaren ilimi", wanda ya gudana a birnin Landan na kasar Burtaniya.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran ma’aikatar ilimi ta Najeriya, Ben Goong ya fitar, shugaba Buhari, ya kara jaddada kokarin gwamnati na tabbatar da karin kaso 50 cikin 100 a kudadden da ake ware wa fannin ilimi a kasar a cikin shekaru biyu.

Haka kuma karin zai iya kai har zuwa kashi 100 bisa 100 nan da shekaru biyar wato daga shekarar 2021 zuwa 2025.

Buhari ya kuma lashi takobin yin aiki da jihohin kasar 36 hade da babban birnin tarayya Abuja, domin tabbatar da samun ci gaba, ta hanyar tabbatar da yin amfani da sama da kashi 20 cikin 100 na kasafin kudi da ake ware wa bangaren ilimi domin cimma nasarar a tsarin daidaituwar ilimi a fadin Najeriya.

Gwamnatin Najeriyar na kuma duba yiyuwar yin kari kan harajin ilimi da kaso 2 zuwa 3 cikin 100 domin kula da tsarin ilimin jami’o’in kasar tare da yin kari a asusun haraji da ake samu ta fuskar tattalin arziki wato CRF don tallafawa ilimin firamare da sakandare daga kaso 2 zuwa 4 cikin 100.

Shugaba Buhari ya kuma sha alwashin kawo karshen matsalar yara da ba sa zuwa makaranta ta hanyar tabbatar da samun ilimi ga yara miliyan 10 da ba sa makaranta a halin yanzu.

Ya kuma ce za'a bunkasa fannin koyar da sana’o’in hannu ga yan Najeriya, da kuma aiwatar da shirye-shirye kan ilimin bai ɗaya, ilimin yara mata, Ilimi na musamman, ilimi ga masu yawan shekaru da kuma shirye-shiryen makarantu na musamman wadanda za su ba da fifiko kan inganci da kima ga kammala karatun firamare da sakandare da dai suransu.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG