NIJAR: Kotu Ta Dage Ranar Shari'ar 'Yan Gwagwarmaya

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Wata kotun birnin Yamai ta dage shara’ar da ya kamata a yiwa wasu jami’an fafitika a jiya talata ba tare da bayyana dalilanta na daukar wannan mataki ba lamarin da ya fara haddasa shakku a wurin lauyoyin dake karesu.

Farfajiyar kotun ta birnin Yamai cika makil da dimbin jama’a a ranar talata domin nuna goyon baya ga Ali Idrissa Nouhou Arzika Moussa Tchangari da Me Larwana Abdurahaman wadanda ya kamata su gurfana a gaban alkali bayan shafe kwanaki 100 a gidajen yarin yankin Tilabery sakamakon zargin gudanar da haramtaciyar zanga zanga, sai dai aka dage wannan zama zuwa ranar 10 ga watan da muke ciki saboda wasu dalilan da ba a bayyana ba inji wani lauyansu Mahaman Rabi'u Umaru.

Faruwar wannan al’amari ya fara jefa shakku a zukatan lauyoyin dake kare wadanan ‘yan gwagwarmaya…

Me Dauda Samna jagoran lauyoyin dake kare wadanda ake zargi a taron maneman labaran da suka kira ya nemi sanin ko akwai maganar boye boye ne a kotu, yace "wace irin gaskiya ce da ba ta faduwa a mashara’anta ?" ya ci gaba da cewa rantsuwar da suka yi kafin fara aikin lauya ba za ta bari su zuba ido ana zubarda kima da mutuncin tsarin shara’ar wannan kasa ba saboda haka yace zasu dage haikan domin kare wannan fanni.

Hukumomi sun bayyana cewa, rashin lakantar abubuwan dake kunshe a takardun wannan shara’a ya sa lauyoyin dake kare ma’aikatar magajin garin Yamai nuna bukatar a basu dama domin harhado bayanai da hujojin da zasu gabatarwa alkali, dalili kenan injisu, da kotun ta dage wannan zama zuwa makon gobe matakin da ya sa lauyoyin dake kare wadanda ake zargi shakku akan yiyuwar ci gaban wannan shara’a akan lokacin da ake fata.

Kama 'yan Fafatukar

An kama wadannan 'yan fafatukar ne yayin wata zanga zangar da ta gudana a ranar 25 ga watan Maris a birnin Yamai, lokacin da suke nuna adawa da dokar harajin 2018 wace suke zargi da jefa talakawan Nijer cikin tsadar rayuwa a wani lokacin da talauci yayi wa kowa katutu..yayinda kungiyoyin ke cewa suna morar ‘yancin da doka ta basu, ita kuwa gwamnatin Nijer tana zarginsu da yunkurin tayarda zaune tsaye hadi da laifin kone kone da farfasa dukiyar jama’a

Saurari rahoton wakilinmu a Niamey Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Shari'ar 'yan gwaggwarmaya-2:55"