A Jamhuriyar Nijar, an yi bikin bude wani taron kasashen Afirka a karkashin inuwar kungiyar UPF ( Universal Peace Federation) da nufin tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya a wannan nahiya da kasashen duniya.
Shugabannin kasashe 6, da wakilan gwamnatoci 17, da tsofaffin shugabannin kasashe 25 ne suka halarci taron da aka gudana a karksahin jagorancin shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou tare da shugabar kungiyar wanzar da zaman lafiya ta FPU, Dr. Hak Ja Han ta kasar Korea ta Kudu, da nufin samarda zaman lafiya a Afirka.
Dukkan kasashen da ke cikin wannan tafiya sun yi amannar cewa, lokaci ya yi, da za a sake daura damara domin tunkarar matsalolin da ke addabar al’umomin Afirka.
Muhimmancin shugabannin addinai, da sarakunan gargajiya a wajen al’umma, ya sa kungiyar FPU ta ga dacewar shigar da su a shirin da aka sa gaba.
Rashin kwakkwarar madogara a wajen matasa da ma al’umma baki daya, ita ma, wata matsala ce da Ambasada Rabi’u Akawu na tawagar Najeriya ke ganin dacewar a maida hankali akanta.
A saurari cikakken rohoto cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5