Hukumar na tunatarwa game mahimmancin aikin tantance sahihanci labari kafin a yada don kaucewa cin zarafin wasu sai dai kungiyoyin ‘yan jarida na ganin akwai alamun fice makadi da rawa a kiraye kirayen na CSC.
A sanarwar da ta fitar a game da yanayin da kafafen labarai ke gudanar da ayyukansu a halin yanzu a nan Nijer hukumar sadarawa ta CSC tace lura da yadda wasu suka dukufa da bada labarin kamzon kurege a maimakon gudanar da bincike domin tantance gaskiyar labari. Ya bada misalin wani labarin da jaridar Canard en furie ta ruwaito a wannan mako game da wasu kudade sama da biliion 9 da tace an ware wa matan shuwagabanin kolin kasar nan domin su kashe wutar gabansu wato fonds ploitique. Dr Sani Kabir shine shugabn hukumar sadarwa ta CSC.
Ko akan matsalar tsaron da ake fama da ita a nan Nijer ma kafafe da dama na kaucewa ka’idar yadda ake bada irin wannan labari inji Dr Sani Kabir .
Ko da yake ya yarda cewa akwai kamshin gaskiya a abubuwan da hukumar ta CSC ke kashedi a kansu Sakataren watsa labarai na gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida Maison de la presse Souleymane Oumarou Brah na ganin alamun fice gona da iri a wannan yunkuri.
Hukumar ta lashi takobin buga sanda akan duk kafar da aka samu da laifin baza karya ko yiwa wani kazafi da kuma wadanda ke neman tunzura jama’a a fannin tsaro.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5