Kungiyar ma’aikatan kamfanonin ta alakanta abin da wasu tarin matsalolin da gwamnatin kasar kadai ce ke da hanyoyin warware su koda yake ta yarda cewa ana fama da tangarda game da ingancin wayar sadarwa a Nijar.
Halin zaman dar dar din da ake ciki a wasu yankunan Nijar na daga cikin dalilan da ma’aikatan kamfanonin wayar sadarwa suka ce suna haifar da koma baya a wannan fanni ganin yadda matsalar ke hana isar da kayan aiki a irin wadanan wurare da a daya gefe ke fama da rashin kyawun hanyoyin mota.
Tsadar haraji na daga cikin kalubalen da ke yi wa tafiyar kamfanonin wayar sadarwa tarnaki a Nijar a cewarsu.
Dubban milliyoyin cfa ne hukumar ARCEP ta caji kamfanonin da suka hada da Airtel Niger Moov Africa Zamani Com da Niger Telecom bayan da bincike ya tabbatar da korafe korafen jama’a kan rashin ingancin layin wayar tarho da internet to amma kungiyar ma’aikata ta bukaci a sasanta.
A bisa doka ma’aikatar kudi ta kasa ce ke da alhakin karbar kudaden tarar da hukumar ARCEP ta ci kamfanonin da ta kama da laifin saba ka’idar aiki wadanda ya zama wajibi a zuba a asusun bital mali. Haka kuma Hukumar na da hurumin yin kashedi ko kuma ta bai wa gwamnati shawarar dakatar da aikin kamfanin wayar sadarwa har ma ta kai ga janye lasisi idan girman laifi ya tsananta.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5