NIJAR: Daukar Matakin Soji Domin Kawar Da Sojojin Da Suka Kifar Da Gwamnatin Farar Hula Ba Ita Ce Mafita Ba - Kungiyar Zabarmawa

Taron Kungiyar Zabarmawa mazauna Najeriya

Kungiyar Zabarmawa mazauna Najeriya ta nuna rashin amincewa da kai harin soja a Nijar bayan juyin mulki da sojoji suka yi a watan Yuli.

A Wani babban taron da kungiyar ta gudanar a birnin Lokoja fadar gwamnatin jihar Kogi a Najeriya, kungiyar tace aukawa Sojojin kasar ta Nijar ba karamar illa bace, domin kuwa ba’a san inda lamarin zai tsaya ba.

Shugaban kungiyar wadda ake kira Zabarkana Alhaji Aliyu Abubakar, wanda ke kula da jihohin kudancin Nigeria 17 yace, suna kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da yayi taka tsan tsan game da wannan fitina da ake son cinnowa, yace, ya kamata a sani cewa, a Nijar akwai Iyaye, da ‘ya‘ya, da yan’uwa, da kakanni da sauran dangi, don haka bai kamata akai wannan shawara a gaban Majalisa ba, ta cewa ana son kai harin soji cikin Nijar.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Ko baya ga batun kasar ta Nijar, kungiyar Zabarmawan tace tana kokarin wayar da kan yan kungiyar akan zaman lafiya, da illar zaman banza, da muhimmancin bin dokokin kasar da ba tasu ba, kamar yadda shugaban kungiyar reshen jihar Naija, Alhaji Muktar Mika’ilu wanda ya kasance a wurin taron ya shaidawa Muryar Amurka.

A bayanin da yayi a wurin, yayi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su zauna lafiya, su hada kai, su yi aiki tare, da yin duk wani abu da zai tabbatar da zaman lafiya. Ya kara da jan hankalin ‘yan kungiyar da su kiyaye duk wata sana’a da ta saba dokokin tarayyar Najeriya, domin tsare mutuncin kansu da dana kasar Nijar.

Batun hadin kan ‘yan kasar ta Jamhuriyar Nijar dake zaune a Nigeria, na daya daga cikin dalilan kafa kungiyar ta Zabarmawa, kamar yadda Alhaji Attahiru Abdullahi Suguru, Shugaban kungiyar reshen jihar Kogi ya fada.

Ya kara da cewa, kowane Bazabarmen da ya shigo Nigeria ya zama wajibi ya hada kai da yan kasar, kuma yasan cewa, ko wane Bazabarme dan’uwan Bazabarme ne, kamar yadda aka sansu da hadin kai da zaman lafiya tsakanin su da juna.

‘Yan kabilar Zabarmawan da suka hada da mazauna Najeriya, da Nijar, sunyi fatar warware takkadamar ta Jamhuriyar Nijar, cikin ruwan Sanyi.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: Daukar Matakin Soja Domin Kawar Da Sojojin Da Suka Kifar Da Gwamnatin Farar Hula Ba Ita Ce Mafita Ba - Kungiyar Zabarmawa