NIJAR: Boko Haram Ta Fara Kashe Mutane A Yankin Tafkin Chadi

Kungiyar Boko Haram

Dubun dubatar manoma da masu kamun kifi a tafkin Chadi ne ke gudun hijira daga tafkin zuwa wasu biranen jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, bayan cikar wa’adin da kungiyar boko haram ta basu domin ficewa.

A ranar Jumma’a ne wa’adin da kungiyar ta boko haram ta bai wa manoman da masu kamun kifi a tafkin na Chadi ya cika domin barin tafkin.

Wannan shine karo na biyu da kungiyar boko haram ke bai wa manoman da masu kamun kifi a tafkin Chadin umurnin barin tafkin.

Sai dai a wannan karo kungiyar ta tsannanta umurnin ta hanyar barazanar hallaka duk wanda bai bar tafkin ba, idan wa’adin ya cika.

Hakan ya sa dubun dubatar manoman da masu kamun kifi ke gudun hijira daga tafkin na Chadi zuwa wasu biranen jihar Diffa.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijira da suka nemi a sakaya sunayensu, sun shaidawa Muryar Amurka cewa, mutane suna ta tururuwa kamar an taso daga masallacin idi, ba dare ba rana ake tafiya, inda mutane suka kwana suna tafiya.

Kuma suna cikin tafiya suka ci karo da mutane biyu an yankasu a kan hanya, bayan sun wuce wannan kuma suka sake cin karo da wasu bakwai an kashe su.

Shugaban kungiyar masu sana’ar kamun kifi a jihar Diffa, Malam Madu Ibrahim, ya ce wannan al’amarin zai iya kawo babbar illa ga kasuwancin kifi a jihar Diffa da ma Tarayyar Najeriya.

A nasa bangaren, Mara Mamadou, daya daga cikin masu fashin baki kan al’ummran yau da kullum a jihar ta Diffa, ya ce wannan al’amarin na iya mayar da hannun agogo baya a kokarin da hukumomin Nijar ke yi wajen tabbatar da tsaro a duk fadin jihar ta Diffa.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin hukumomin jihar Diffa game da wannan al’amarin, amma haka bai samu ba.

Saurari cikakken rahoton Aboukar Issa:

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: Boko Haram Ta Fara Kashe Mutane A Yankin Tafkin Chadi