A jamhuriyar Nijer ‘yan takarar da zasu fafata a ranar 21 ga watan fabreru sun fantsama zuwa sassan kasar domin neman goyon bayan talakkawa .
A yayinda Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya ya kaddamar da yakin zabensa a jiya lahdi a birnin yamai shi kuwa dan takarar jam’iyun hamayya Mahaman Ousman ya gudanar da gangaminsa na farko a garin Tilabery.
Irin yadda magoya bayan jam’iyun kawancen Coalition Bazoum 2021 suka cashe a jiya lahdi kenan a nan yamai a yayin gangamin kaddamar da yakin zaben dan takarar jam’iyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed.
Bazoum Mohamed yace "sakamakon zaben ‘yan majalisar dokoki ya yi nuni da cewa jam’iyar PNDS da kawayenta na da rinjaye a sabuwar majalisar dokoki domin muna da kujeru 129 daga cikin kujerun wakilci 166. idan aka yi la’akari da haka ba zai zama laifi ba idan muka ce zamu lashe wannan fafatawa abin nufi zaben 21 ga watan fabreru a garemu tamkar cika sunna ne to amma kuma irin wannan tunani kuskure ne babba kadda mu sa a kanmu cewa kokowa ta kare."
A nasa bangare dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman ya kaddamar da yakin zabe a jiya lahadina garin Tilabery inda magoya bayan kawancen CAP 20 21 suka gudanar da gangami.
A na sa jawabin Mahaman Ousman ya bayyana cewa:
yanayin tabarbarewar tsaron da ake ciki a yankin Tilabery ne ya sa na yanke shawarar kaddamar da yakin zabe a nan. a bayyane take gazawar hukumomi a fannin tsaro a ‘yan shekarun nan ta jefa al’umomin jihohin Tilabery da na Diffa da na Tahoua cikin kuncin rayuwa sakamakon rashin samar da kayan aikin da suka dace wajen yakar ‘yan bindigar da suka addabi jama’a lamarin a dai bangare ke jefa dakarun tsaro da fararen hula cikin halin rashin wata kariya daga barazanar irin wadanan ‘yan takife da ke kai hare hare ba kakautawa a wadanan yankuna inda ake ta fuskantar asarar dimbin rayukan bayin Allah."
A yau litinin dan takarar PNDS Bazoum Mohamed ya bakunci jihar Tilabery yayinda ajandar Mahaman ousman na RDR Canji ke nunin dan takarar zai ziyarci jihohin Zinder da Maradi daga ranar 8 zuwa 14 ga watan fabreru.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5