Ta bangaren ruwa cikin makon da ya gabata aka rufe famfon dake basu ruwan sha dalili ke nan suka koka domin a taimaka masu.
Mutane da dama suna kwana ne wurin famfaon ruwa suna jira su samu su diba su kai gidajensu, wasu ma wai sun kai kwana uku a famfaon..
Mutanen dake garin Cancandi dake kokawa da karancin ruwa da na abinci 'yan gudun hijira ne da rikicin Boko Haram ya daidaita.Ko su ainihin mazauna garin suna fama da karancin ruwa lamarin da ya sa wasu suna barin garin.
Wani bafillace yace shanunsa sun yi kwana uku basu samu ruwan sha ba. Sun yi kuka amma gwamnati tace tana yin gyara ne, batun da shi yayi shakka a kai.
Matsalar ruwan ta samo asali ne da karin jama'a da garin ya samu sanadiyar 'yan gudun hijira. Adadin jama'ar garin dubu uku ne amma yanzu sun kai dubu tara. To saidai gwamnati tace ta kawo famfuna kuma zata yi kokarin yin gyara domin a kawar da matsalar.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5