Banda cikas da matakan yaki da annobar corona suka haddasa wa ‘yancin jama’a a shekarar ta 2021, hukumar tace matsalolin tsaron da ake fama da su a jihohin Diffa da Maradi da Tilabery da Tahoua sun janyo tauye wa jama’a hakkoki fiye da kima inda aka gano cewa, an yi satar mutane a kalla sau 311 lamarin da ya shafi farar hula 754 ya kuma rutsa da jami’an tsaro 136. Wannan matsala ta hana dalibai 65,552 zuwa makaranta yayinda aka rufe asibitoci kusan 80 a yankunan dake fama da tashe tsahen hankula .
Haka kuma a shekarar ta 2021 hukumomi a wasu manyan da’irori sun hana jama’ar morar ‘yancin gudanar da gangami ko zanga -zanga sannan an yi ta kama ‘yan jarida da jami’an fararen hula sannan rikicin zabe ya haifar da garkame ‘yan siyasa da dama har ma da gurfanar da wasu daga cikinsu a kotu a bisa zarginsu da aikata ayyukan ta’addanci.
Dokar hana amfani da babura a yankunan da ake fuskantar aika aikar ‘yan bindiga na daga cikin matakan tauye hakkin dan adam da aka yi fama da su a 2021 saboda yadda abin ke hanawa jama’a kai da kawowa, sannan ta wani bangare tamkar take ‘yancin gudanar da sana’a ne.
Hukumar ta yaba da abinda ta kira matakan da gwamnatin Nijer ta dauka a tsawon shekarar da ta gabata da nufin murkushe matsalolin tsaro . Sai dai a cewar dan majalisar dokokin kasa daga bangaren ‘yan hamayya Hon Omar Hamidou Tchana akwai alamar tsambare a tattare da wannan rahoto.
Hukumar ta CNDH wace kundin tsarin mulkin kasa ya wajabtawa gabatar da rahoton ayyukanta a kowace shekara a gaban Majalisar dokokin kasa ta zo da wasu shawarwari a karshen wannan rahoto ko da yake ta ce ta gano yadda ake buris da shawarwarin da take bayarwa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5