Hukumomin jihar Diffa a Jamhuriyyar Nijar sun tabbatar da sahihancin tubar wasu 'yan Boko Haram su 54, bayan binciken wata daya aka yi masu a cibiyar gyara halinka dake garin Gudumariya.
Shugaban hukumar dake kula da wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyyar Nijar, Janar Abou Tarka, shi ne ya jagoranci bikin sallamar tubabbin 'yan Boko Haram din tare da halartar gwamnan jihar diffa Issa Lemine.
'Yan boko Haram din 54 da aka sallama, akasarinsu matasa ne, kuma yan assalin jihar diffa.
Kawo yanzu dai yan Boko Haram kimanin 500 ne suka mika wuya tun bayan da hukumomin Nijar suka yi kira ga yan Boko Haram din da cewa su mika wuya kuma gwammanti zata dauki matakan kulawa da su a a shekarar 2017.
Ganin cewa, tubbabun ‘yan Boko Haram din da aka sallama ba su jima ba a cibiyar gyara halinka, ko hakan bai zai sa al’umma ta rika dari dari da su ba? tambayar kenan da masu amsa ta su ka ce, ai an tabbatar da gaskiyar wannan tuba.
Ana dai sa ran ‘yan Boko Haram da dama zasu mika wuya a nan gaba, sai dai tubbabun ‘yan boko haram sun yi kira ga hukumomin Nijar da su kara daukar matakan kyautata masu.
Saurari cikakken rahoton Aboukar Issa:
Your browser doesn’t support HTML5