Nijar: An Kammala Taron Tsoffin Shugabannin Afirka

Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

A karshen wani taron kwanaki 3 da suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar tsofaffin shugabannin kasashen Afirka, da na kungiyoyin fararen hula sun kudiri aniyar soma tuntubar shugabannin kasashe akan mahimancin mutunta ka’idar wa’adin mulki, dai dai abinda kundin tsarin mulki ya yi tanadi, a ci gaba da neman hanyoyin karfafa demokardiyya a wannan nahiya.

Madam Chantal Nare ta Burkina Faso ta gabatar da sanarwar karshen taron tsofaffin shugabannin kasashen Afirka, bayan shafe kwanaki 3 ana tattauna hanyoyin magance matsalar kwaskware kundin tsarin mulki..

Taron ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka da sauran kungiyoyin kasa da kasa irinsu ECOWAS, da makamantansu dasu dage haikan don ganin an mutunta abubuwan dake rubuce a kundin tsarin mulkin kasa, sannan aka gargadi shugabanni dasu guji kwaskware kundin tsarin mulki ta hanyar amfani da karfi, domin kaucewa barkewar rigingimun da aka saba fuskanta a wannan nafiya.

Tsohon shugaban kasar Nijar Alhaji Mahaman Ousman na kallon wannan yunkuri na cibiyar NDI a matsayin wata hanyar kawo karshen zagon kasar da demokradiyya ke fuskanta a ‘yan shekarun nan a nahiyar Afirka.

Shi kuwa a nasa bayanin, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace sauka daga karagar mulki salum alum bayan shudewar wa’adi, ko bayan cin nasara a zabe wani abu ne dake karawa 'yan siyasa daraja a idon Duniya.

Masu rajin kare demokradiyya sun dauki alkawarin kaddamar da zagaye a kasashen da shugabanninsu ke kokarin shirya tazarce ta haramtaciyar hanya irinsu Guniea, da Conacry, da Cote d’ivoire, da kuma Cameroun, da nufin tayarda talakawa daga barci domin tilastawa shugabaninsu daraja.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: An Kammala Taron Tsoffin Shugabannin Afirka