Tuni dai jami’an tsaro suka cafke dan fashin wanda shi ma jami’in tsaro ne dake aiki a gundumar Abala ta jihar Tilabery lamarin da ya sa jama’a ta fara jan hankulan mahukunta a game da yadda sha’anin tsaro ke kara lalacewa a birnin yamai.
Lamarin ya faru da rana kiri kiri a unguwar Tallague daya daga cikin unguwanni mafi yawan jama’a a birnin Yamai inda wani mutun dauke da bindiga kirar PA wato pistolet ya kai farmaki a reshen kamfanin aika sakwannin kudi na Zeyna inda ya yi nasarar kwace 815000 na cfa sai dai lokacin da ya yi kokarin arcewa ma’aikaciyar wurin ta damke shi ta wuya ta yi ta kururuwar neman agaji daga jama’a mafari kenan aka yi wa wannan barawo kofar rago kafin isowar jami’an tsaro wadanda a take suka tasa keyarsa zuwa ofishin ‘yan sanda.
Binciken farko farko na nunin wannan dan fashi jandarma ne mai sunan Alassane nouhou dake aiki a gundumar Abala ta jihar Tilabery haka kuma an kama shi dauke da karamar bindigar hannu da harsasai kimanin 14.
Samun jami’in tsaro da aikata irin wannan danyen aiki wani abu ne da ke daure kai inji Alhaji Salissou Amadou na kungiyar Sauvons le Niger.
Ko a karshen makon da ya gabata ma wani dan fashi ya afkawa irin wadanan gidajen aika sakwannin kudade a unguwar Koubia dake Yamai inda ya harbi mai kula da wurin a kafafuwanta kafin ya bi kara.
Fashi da makami wani abu ne da ke kokarin samin gindin zama a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijer inda a watannin baya wasu ‘yan bindiga suka afka wa wani shagon saida karfen zinare kuma a haka a karshen shekarar da ta gabata ‘yan fashi sun kwace milyon 600 na CFA mallakar wani dan kasuwa lokacin da ake kan hanyar kai su ajiya a banki ba’idin sace da sace da fashin da ake yi wa mata a kewayen kasuwani ko cikin motocin haya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5
Binciken farko farko na nunin wannan dan fashi jandarma ne mai sunan Alassane nouhou dake aiki a gundumar Abala ta jihar Tilabery haka kuma an kama shi dauke da karamar bindigar hannu da harsasai kimanin 14.