Mahakaran sun shigo garin ne a cikin dare inda suka cinnawa garin wuta suka kuma fara harbin kan maii uwa da wabi da nufin kashe mutanen da zasu yi kokarin ceton rayukansu daga gobarar da ta tashi. Magajin garin Boso Alhaji Bako ya bayyana cewa, mutane bakwai suka muta a harin yayinda aka kona motoci goma sha daya.
Wadansu da aka yi hira da su sun bayyana cewa, maharan sun shiga garin ne da misalin karfe goma sha daya na daren suka bude masu wuta. Bisa ga cewarsu, maharani sun kai kimanin dari biyu da shigarsu kuma saka fara kone kone.
Wani da sashen Hausa ya yi hira da shi ya bayyana cewa, shi kanshi gidanshi ya kone kurmus. Yace lamarin yayi muni ainun kuma kawo yanzu ba za a iya kimanta asarar da aka yi ba.
Ana kuna zaton cewa, maharan d ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun zuba guba a rijiyoyin garin.
Ga rahoton da wakiliyar Sashen Hausa Tamar Bari ya aiko daga Damagaran.
Your browser doesn’t support HTML5