Nijar: An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafawa Jama'ar Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Nijar: Ambaliyar Ruwan Kogin Komadougou A Yankin Diffa

Dubban mazaunan garuruwa da dama na yankin Diffa ne Kogin Komadougou ya tilastawa tashi daga gidajensu sakamakon boren da kogin ya tayar a watan Oktoban da ya gabata, lamarin da ya salwantar da dimbin gonakin shinkafa da na tattasai.

Wannan lamari ya jefa jama’a cikin halin kaka nika yi da har yanzu ba su murmure ba daga matasaloli masu nasaba da rikicin Boko Haram, mafari ke nan da kungiyar jinkai da ayyukan ci gaba mai dorewa APPED ta bude wata gidauniya domin wadanan mutane.

Shugabar kungiyar APPED, Mariam Djibril, tace irin hali da suka jama’a suka shiga shine ya zaburar da su suka ga ya kamata su nemi jama’a da su taimaka wajan tallafawa wadanda wannan bala’i ya shafa.

Sai dai da alama dai kiran wadanan matasa ya shiga kunnuwan jama’a.

Jagororin wannan yunkurin na kungiyar APEDD sun yi alkawalin isar da tallafin da suka samar a hannun wadanda aka yi abin domin su.

Bayan zaman wuni biyu karshen makon nan a Otel Radison Blu, za a ci gaba da karbar gudunmowar al’uma a cibiyar kungiyar APPED da ke birnin Yamai har zuwa ranar 20 ga watan nan na Nuwamba.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Souley Moumouni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar-An Kaddamar Da Gidauniyar Tallafawa Jama ar Da Ambaliyar Ruwan DiffaTa Shafa