Nijar: An Gudanar Da Wani Taro Da Nufin Bullo Da Hanyoyin Ceton Matasa

Taron Dattawan Yankin Zinder A Binin Yamai

A jamhuriyar Nijar, Damagarawa mazauna birnin Yamai da kasashen waje sun gudanar da taro a birnin Yamai a karkashin jagorancin mai martaba Sultan Abubakar Sanda inda aka kaddamar da ayyukan wani kwamiti da ke da nauyin tunkarar matsalolin da ke addabar wannan Yanki.

Kwamitin mai suna CADRZ a takaitace ainihinsa wasu matasa ‘yan takarda ‘yan asalin jihar Zinder da ke zaune a ciki da wajen kasar Nijar ne suka kafa shi da zummar gudanar da ayyukan da za su taimaka a fitar da yankin Damagaram daga halin tabarbarewa.

Sultan Aboubacar Sanda A Taron Dattawan Yankin Zinder Birnin Yamai

Mai martaba sarkin Damagaram Sultan Abubakar Sanda da ke shugabancin taron ya yaba da wannan shiri, sannan ya gargadi daukacin Damagarawa su kiyayi dukkan ababen da ka iya bata tsari.

Dattawan yankin Zinder irinsu tsohon ministan cikin gida Idi Ango Omar sun jaddada aniyar bada gudunmowar da ta dace don ganin an cimma burin da aka sa gaba.

Taron Dattawan Yankin Zinder A Binin Yamai

Daga karshe kwamitin na CADRZ ya sanar cewa zai soma gudanar da ayyukansa gadan gadan daga farkon watan Janairu na shekarar 2020.

Ga rohoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: An Gudanar Da Wani Taro Da Nufin Zakulo Hanyoyin Ceton Matasa