NIJAR: 8 Ga Watan Maris Ranar Mata Ta Duniya

Zanga Zangar Kungiyoyin Mata Kan Fyade

Ranar takwas rana ce ta tunawa da gudunmowar da mata ke badawa, wadda Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don duba matsaloli, koke koke da bukatun mata na duniya

Tun faruwar wannan rana mata ke gwagwarmaya kan tabbatar da hakkinsu a fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, siyasa, kasuwanci da dai sauransu musamman a irin wannan yanayi.

Niger Kungiyoyin Mata

Kowace shekara ana daukar maudu'i mai nasaba da matsalolin mata; a bana an maida hankali kan yaki da cutar covid 19, inda a nan Damagaram kungiyoyin mata suka gabatar da irin gudumuwar da suka bayar kamar waye kai, bada kayayakin kariya da sauransu.

Sputnik V - Rigakafin cutar COVID-19

Irin kokarin da kungiyoyin mata da ma wasu matan suka kawo game da yaki da covid 19 a jahar Damagaram ya kai hukumar jaha ta kiwon lafiya ta jinjina ma mata ta bakin daraktanta Abu Yahya bisa muhummiyar rawar da suka taka wajen yaki da cutar covid 19.

Ga wakiliyarmu daga Damagaram Tamar Abari da rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

NIJAR: 8 Ga Watan Maris Ranar Sallar Mata Ta Duniya