Wasu jam'iyyun da suka goyi bayan shugaban kasa Issoufou Mahammadou na PNDS Tarayya a zaben zagaye na biyu da ya bashi nasara suna murna da nadin sabbin ministoci 38 da suka hada da nasu mutanen.
A cewar Abdulwahab Garba kakakin jam'iyyar CDS Rahama reshen birnin Kwanni a nasu bangaren kwalliya ta biya kudin sabulu.Yace duk mutanen da suka goyi bayan tafiya da shugaban kasa kowa a bashi nashi kaso daidai gwargwado. Ya kara da yiwa kasar ta cigaba domin basu da wata kasa da suke tinkaho da ita da ta wuce Nijar.
Haka ma a bangaren jam'iyyar NPR Jamhuriya ta Albade Abuba reshen birnin Kwanni Alhaji Sani Maikaset na cewa nadi ya yi domin duk wanda aka sa ya dace da matsayin da aka bashi.
Amma a ganin wani matashi Malam Abdallah ministocin sun yi yawa. Yace har yanzu Nijar karkashin Faransa take kuma ko ita Faransar ministoci 16 gareta duk da cewa tanada al'umma miliyan 66 yayinda Nijar ke da mutane miliyan 19 kacal.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5