Ko baya ga tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya Air Chief Alex Badeh, da ‘yan kwanakin na hukumar EFCC, ta kwace wani dangareren gidan sa dake Wuse 2, a birnin Abuja, kuma ke fuskantar bincike.
Kazalika, akwai kuma Karin wasu manyan Sojoji, da a baya bayan nan aka gano suna da hanu dumu dumu a badakalar kudaden sayen makamai da ya faru tsakanin 2007 zuwa 2015.
Wadannan manyan hafsoshi da a halin yanzu suke cikin khaki ka iya rasa mikamaman su dan fuskantar amintatcen bincike sune Air vice Marshall A.M Mamu, Air Vice Marshall Oguntoyibo, Air Vice Marshall T Omeniyi, Air Vice Marshall J.B Adigun da Air Vice Marshall R.A Ojo.
Sauran sun hada da Air Vice Marshall Kayode Barkley, Air Commodore Ogun Jobi, Air Commodore G.M.B Gwani, Air Commodore S.O Makinde, Air Commodore A.Y Lasa, da kuma kanal N Ashinze.
Cikin hafsoshi 11, guda 10, daga rundunar mayakan saman Najeriya suke, wani tsohon Sojan saman Najeriya, Air Commodore Baba Tijani Gamawa, yace har yanzu rundunar Sojojin sama na cikin hukumar da take samun kulla, matukar shuwagabani suka ji tsoron Allah sukayi abubuwa abisa ka’ida dukkan wadannan abubuwa zasu tafi dai dai, amma wani lokaci shugabanin sukan kauce hanya saboda wasu biyan bukatu na kansu.
Your browser doesn’t support HTML5