Kusan dukkan wasu masu bakin fada a ji a game da harakokin shara’a da jam’ian kare hakkin dan Adam daga kasashen Afirka ta yamma da na yankin Sahel ne ke halartar wannan mahawara dake gudana a karo na biyu domin tattaunawa akan illolin rashin hukunta masu laifuka..
Shugaban kungiyar yaki da cin hancin reshen Transparency International a Niger Mamman Wada ya yi karin bayani akan mahimmancin wannan haduwa. Ya ce idan wani ya dauki abu na wani ba'a yi komi ba ko kuma wani an kutunta mashi ba'a yi masa shari'a ta gaskiya ba, ire-iren hakan ne ke kawo tarzoma a cikin kasa. Da zara tashin hankali ya faru kuma mata da yara ne ke fadawa cikin mawuyacin halin.
Shugaban kasar NIger Issoufou Mahamadou a jawabinsa na bude taron cewa ya yi...
"Rashin hukunta masu laifuka wani abu ne da ya juyawa dukkan wani shirin zaman lafiya baya saboda haka ya zama wajibi hukunci ya hau kan dukkan masu hannu a faruwar irin wannan mummunar dabi’a yayinda ya zama dole a biya diyya wa mutanen da aka taoyewa hakkoki…
Cin nasarar irin wannan yunkuri wani abu ne da ya danganta da yadda gwamnatoci ke maida hankali akan batun mutunta doka da yaki da cin hanci yayinda a daya bangaren ya dace a karfafa aiyyukan ci gaban al’umma"
Kwanaki 3 za a shafe ana gudanar da wannan taro da ke samun halartar wakilin sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD a Afirka ta yamma Mohammed Ibn Chambas da wakilyar kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka da na kungiyar ECOWAS wanda a karshe zai zo da shawarwarin da zasu taimaka a dauki matakan mutunta ‘yancin dan Adam a Afirka ta yamma da yankin Sahel.
A saurari rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5