Mohammed, shine wakilin kungiyar PROMAB ta jamhuriyar Nijer, kuma yayi karin bayanin cewa kungiyar ta mayar da hankali ne wajan ayyukan noma, musamman ta fannin da ya jibanci bada horo da tallafi da kuma bada shawarwari ga manoma da kungiyoyi.
Ya kara da cewa suna aiki kafada da kafada da gwamnati domin taimakawa hukumar dake kula da harkokin Noma na gwamnatin kasar Nijer, cikin tsare tsaren ta na inganta harkokin noma.
Mohammed, ya bayyana cewa kungiyar ta fara aiki tun daga shekarar 2012, dan haka a cikin shekaru biyar da kungiyar ta kwashe tana gudanar da wadannan ayyuka ta sami nasarori da dama, kama daga ba manoma horo da tallafi ga mata masu sana'ar sarrafa kayayyakin gona.
Cikin kayayyakin aikin da wannan kungiya ta bayar sun hada da Tantan da injinan busar da anfanin gona da tamfal da sauran su
Saurari rahoton Tamar Abari domin cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5