Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chadi Ta Yi Mamakin Saka Ta Cikin Kasashen Da Aka Hana Ma Zuwa Amurka Cikin Sauki


Shugaba Idris Deby na Chadi yana jawabi gaban taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Idris Deby na Chadi yana jawabi gaban taron Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Chadi ta yi mamakin saka ta da Amurka ta yi cikin jerin kasashen da aka haramta ma mutanensu zuwa Amurka ba tare da matakai masu tsauri ba. Gwamnatin kasar ta ce ita fa ba ta fahimci musabbabin saka ta cikin jerin kasashen da aka tsaurara masu sharuddan shiga Amurka ba.

Bayyanar sunan kasar Chadi a cikin jerin sabbin sunayen da Amurka ta fitar na wadanda aka haramtawa shiga kasar ya jefa Chadin cikin mamaki.
A wata sanarwa da Ministar sadarwar kasar ta fitar da harshen Faransanci, Madeleine Alingue, ta ce gwamnatin ta Chadi, ba ta fahimci dalilin da ya sa aka saka sunanta a jerin sunayen kasashen da aka haramtawa shiga Amurkan ba.
A ranar Lahadin da ta gabata, gwamatin Shugaba Trump ta fidda sabbin ka’idojin shiga kasar, wadanda aka dora su akan na farko da aka gindaya a watan Maris din da ya gabata, wadanda suka haramtawa wasu kasashe shida, masu mafiya rinjayen Musulmi shiga Amurka.
Sabbin ka’idojin sun hada da kasashen Venezuela da Korea ta arewa da kuma Chadi.
Jama’a da dama sun nuna mamakinsu da aka saka sunan Chadi cikin jerin sunayen, domin kasa ce da ta kasance kawa ga Amurka wajen yaki da ayyukan ta’addanci.
Baya ga haka, Amurka ta sha jagorantar atisayen yaki da ta’addanci a kasar, tare da horar da dakarunta, wadanda ake musu kallon babu kamarsu wajen kwarewa a yankin tsakiyar Afirka.
Ita dai Chadi tana tsakiyar wani yanki ne mai tsauri, zagaye da kasashe irinsu Libya da Sudan da Najeriya da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Sabbin ka’idojin sun nuna cewa kasar ta Chadi ba ta ba da bayanan da suka shafi kare lafiyar jama’a da yaki da ta’addanci.
Har ila yau ka’idojin sun nuna cewa akwai kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama a kasar ko a kewayenta da suka hada da Boko Haram da reshen kungiyar ISIS dake yammacin Afirka da na Al Qa’ida da ke yankin Islamic Maghreb.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG