NIGER: Hukumar CNUT Ta Kaddamar Da Aikin Wayar Da Kan ‘Yan Kasuwa

Wasu makiyaya na kallon ramammun dabbobin su, na kalace-kalacen abinci a kasa a wata kasuwar Dakoro a kasar jamahuriyar Nijer.

Hukumar kula da fitar da kayayakin ‘yan kasuwar Nijer a tashoshin jiragen ruwa, CNUT, ta kaddamar da aiyukan fadakarwa don kaucewa matsalolin kan hanya a wannan lokaci da yakin Russia a Ukraine ke haddasa tsaiko ga harkar sufuri.

La’akari da wahalhalun da ‘yan kasuwar Nijer masu shigar da kaya daga kasashen waje ke fuskanta, ya sa gwamnatin kasar kafa hukumar Conseil Nigerien des Utilisateurs des Transports CNUT don ba su kariya daga matsalolin da ka iya tasowa.

Malan Yazi Abdou dake zaman jami’in hukumar, ya ce ganin yadda har yanzu ‘yan kasuwa da dama ba su da masaniya a game da alakar aikin dake tsakaninsu da CNUT musamman a jihohi ya sa hukumar kaddamar da aiyukan tuntuba da fadakarwa.

Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar Import Export Chaibou Tchombiano, wanda ya nuna gamsuwa da shawarwarin ya kuma bada shawarar karawa wannan hukumar karfin, ganin yadda take sa ido tun daga fitowar kaya har zuwa cikin ‘kasa.

Jamhuriyar Nijer dake tsakiyar yankin sahel na fama da tarin kalubale wajen shigo da kayayaki, sakamakon rashin tashar jirgin ruwa lamarin da ke shafar sha’anin kasuwanci saboda wahalwalun kan hanya masu nasaba da harkokin dakon kaya, dalilin da ya sa hukumomin kasar kulla yarjejeniya da kasashe makwafta dake gabar teku, to amma duk da haka har yanzu da sauran rina mafarin kafa wannan hukuma ta CNUT kenan don kare hakkokin ‘yan kasuwar kasar a ketare.

Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

NIGER: Hukuma CNUT Ta Kaddamar Da Aikin Wayar Da Kan ‘Yan Kasuwa - 3'17"