Wata takarda dake dauke da sa hannun ministan cikin gida na jamhuriyar Nijar wato Hashim Masa'udu ta haramta kawancen FAR.
Takardar tace bayan nazari da gwamnati tayi kawancen bashi kan kaida saboda haka ba halal ba ne.Takardar tace babu dokar da ta bada daman kafa irin wannan kawancen.
To saidai tuni shugabannin FAR suka yi watsi da takardar. Madam Bayar Maryama kakakin kawancen tace ana so ne a yi masu danniya. Matakin na gwamnati take masu haki ne tare da kokarin hanasu yin walwala.
Madam Maryama tace kasar Nijar kasar dimokradiya ce. Tace babu gudu babu ja da baya sai sun cigaba da kawancen. A cewarta harkokin Nijar sun tabarbare. Shekaru hudu da suka gabata sun mayarda kasar baya.
Maryam ta cigaba da cewa cin hanci da rashawa sun yiwa kasar katutu. Cin hanci a keyi na babu kunya ko tsoron Allah.
Zasu cigaba da kokawa saboda kare kasarsu daga fadawa cikin tashin hankali.
Masana dokokin kasar sun ce basu yi bayani ba akan kaidojin kafa kawance tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula. To saidai Dr Abubakar Ahmadu Hassan yace tun ba yau ba aka saba ganin irin kawancen.
Yanzu dai an sa ido a ga yadda zata kaya a daidai lokacin da zabukan kasar ke karatowa.
Ga rahoton Sule Mummuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5