NHRC Ta Samu Rahoton Tauye Hakki 265 A Jihar Yobe

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni

Jami’in dake jagorantar NHRC a jihar yobe, Labaran Babangida, ne ya bayyana hakan yayin bikin zagayowar ranar kare hakkin dan adam ta duniya ta bana a birnin Damataru, fadar gwamnatin jihar Yobe.

Hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya ta samu rahotannin daban-daban kan cin zarafin bil adama a jihar Yobe har guda 265 daga watan Janairu zuwa Nuwamban 2024.

Jami’in dake jagorantar NHRC a jihar yobe, Labaran Babangida, ne ya bayyana hakan yayin bikin zagayowar ranar kare hakkin dan adam ta duniya ta bana a birnin Damataru, fadar gwamnatin jihar Yobe.

“A bana an samu karuwar cin zarafin bil adama a jihar Yobe. hakan ta faru ne sakamakon wayar da kan jama’ar da aka yi da kuma amincewar da al’umma tayi na neman a bi musu hakkinsu idan an ci zarfinsu,” a cewarsa.

“Daga bayanan da muke dasu a halin yanzu, muna da kimanin rahotannin tauye hakki 265 wadanda suka zarta na bara. A duniya baki daya, matsalar durkushewar tattalin arzikin na daga cikin dalilan da suka sabbaba hakan tare da rikicin dake gudana a jihohin Borno da Adamawa da Yobe, dukkaninsu sun bada gudunmawa wajen karuwar cin zarafin.”

Ya kuma bukaci gwamnati da ta jajirce wajen kare hakkokin al’umma domin basu kariya.