Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada yau Laraba cewa gwamnatin hadin gwuiwar kasar na nan daram, kuma ya yi watsi da kiran da rundunar ‘yan sandan kasar ta yi cewa a tuhume shi bisa laifukan cin hanci da rashawa.
Netanyahu ya ce babu wanda ke da shirin yin zabe. Ya kuma ci gaba da cewa “za mu ci gaba da aiki tare don neman ci gaban ‘yan Isra’ila" har zuwa karshen wa’adi mulkinsa.
Kiran da aka yi game da tuhume-tuhumen manyan laifuka jiya Talata na zuwa ne bayan watannin da aka kwashe ana bincike akan zarge-zargen cewa Netanyahu ya karbi kyaututtuka masu tsada daga attijarai biyu.
Daga cikin wadanda ake zargin sun ba shi kyauta akwai haifaffen Isra’ila mai aiki a masana’antar fina-finan ta Hollywood a Amurka Arnon Milchan.
Daya attajirin shi ne mutumin nan da ya yi fice a fannin kafafen sadarwa a Australia mai suna James Packer.
Attorney Janar na Isra’ila Avichai Mandelblit ne zai yanke shawara ko za ‘a tuhumi Natenyahu ko kuma akasin haka.