A Tel Aviv, masu zanga-zangar sun tare babbar hanyar birnin, inda suka haifar da hayaniya da ganguna har ma da haddasa gobara.
A birnin Kudus, masu zanga-zanga kusan 1,000 wadanda suka fusata da korar ministan tsaro, sun taru a wajen gidan Netanyahu. An kuma bayar da rahoton wasu zanga-zangar a fadin kasar.
Yayin da Netanyahu ya ci gaba da matsin lamba da sojojin Isra'ila kan Hamas, Gallant ya yi kira da a dauki akalla yarjejeniyar wucin gadi don dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga Oktobar shekarar 2023.
Tun daga wannan lokacin, Isra'ila ta kuma yi ta gwabza kazamin fada da mayakan Hizbullah na kasar Labanon, tare da yin musanyar kai hare-hare masu dogon zango da Iran.
Netanyahu ya fada a cikin wata sanarwa jiya talata cewa amincewar da ke tsakanin Gallant da shi ta kau a tsawon yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.