Netanyahu Ya Kasa Kafa Sabuwar Gwamnati A Isra'ila

Firai Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ya gaza kafa sabuwar gwamnati bayan zaben 'yan majalisar da bai kammalu ba, a watan da ya gabata, lamarin da ya bai wa babban abokin hamayyarsa Benny Gantz, damar yunkurin hada kan 'yan majalisar dokoki masu rinjaye tare da zama da nufin zama sabon shugaban kasar.

Netanyahu, wanda ya kasance Firai Ministan kasar da ya fi dadewa a karagar mulki, na neman yin wa'adi na biyar a matsayin Firayim Minista.

Amma Netanyahu, wanda har ila yau shi ne shugaban jam'iyyar Likud, masu ra'ayin mazan jiya, ya fadawa shugaban Isra’ila, Reuven Rivlin, cewa ya gaza samun rinjayen kujeru 61 a majalisar dokokin kasar ta hanyar kafa gwamnatin hadaka tare da babbar jam’iyyar adawa ta Blue and White, da Gantz ke jagoranta.

Rivlin ya ce, a yanzu zai ba Gantz, tsohon shugaban tsaron Isra’ila, kwanaki 28 don kokarin kafa gwamnati, duk da cewa shi ma yana fuskantar kalubale.

Bisa doka, idan Gantz ya gaza kafa gwamnati cikin kwanaki 28, kowanne dan majalisa na iya kokarin kafa gwamnati a cikin kwanaki 21 bayan cikar wannan wa’adin.

Idan kuma haka ya cutura, ya zama ala tilas kasar ta Isra'ila ta gudanar da sabon zaben ‘yan majalisar dokoki na uku cikin watanni shida.