Netanyahu Ya Dakatar Da Shirin Yin Garambawul Ga Sashen Shari’ar Kasar

Frayim Ministan Israila Netanyahu Ya Ce Da Yiwuwar Yin Sulhun Wucin Gadi

A ranar Litinin Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dage shirinsa na yin garambawul a bangaren shari’ar kasar sakamakon zanga-zangar da aka yi a kan titunan kasar.

Dubban masu zanga-zanga ne suka gudanar da zanga zangar nuna adawa da sauye-sauyen da za su bai wa gwamnati karin iko kan harkokin shari’a.

A ranar Litinin Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dage shirinsa na yin garambawul a bangaren shari’ar kasar sakamakon zanga-zangar da aka yi a kan tituna da kuma yajin aikin da ma’aikatan kasar suka yi na adawa da shirin.

Da yake bayyana shi a matsayin hanyar “kaucewa yakin basasa,” Netanyahu ya yi alkawarin tuntuba na cimma yarjejeniya, yayin zaman majalisar wanda zai fara a ranar 30 ga watan Afrilu mai zuwa.

Shirin firai ministan ya bukaci da a kara karfin ikon majalisar dokokin kasar, ciki har da nada alkalai da hakkin soke hukuncin da bata so.

Wannan ya matukar raba kan kasar Yahudawan tare da janyo wasu jama’ar kasar suka ce ba za su yi aikin sojan Isra’ila ba, idan har aka kafa ta, da kuma ikirarin cewa kasar na karkata zuwa ga mulkin kama karya.

A halin da ake ciki, karamin rinjayen da na Netanyahu ya ke da shi a majalisar dokokin kasar sun ci gaba da yin kira da a gudanar da garambawul din.

Da yake sanar da jinkirin, Netanyahu ya ce, “abu daya da ba zan yarda da shi ba, akwai ‘yan tsirarun masu tsattsauran ra’ayi da ke son wargaza kasarmu, wanda babban laifin ne.”

Kafin sanarwar Netanyahu, ma’aikatan Isra’ila sun fara yajin aiki a fadin kasar a ranar Litinin, kuma dubun dubatar mutane sun sake yin zanga-zanga a wajen majalisar dokokin kasar.