Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Naftali Bennett Ya Zama Firai Ministan Isra'ila

FILE - Naftali Bennett, leader of Israel's Yamina (New Right) party, addresses supporters at his party's campaign headquarters in the Mediterranean coastal city of Tel Aviv, March 24, 2021.
FILE - Naftali Bennett, leader of Israel's Yamina (New Right) party, addresses supporters at his party's campaign headquarters in the Mediterranean coastal city of Tel Aviv, March 24, 2021.

Sabuwar gwammnatin Bennet mai ra’ayin mazan jiya, wanda dan jam’iyyar Yamina ne, za ta yi wa’adin shekara biyu.

Naftali Benett ya zama zababben Firai ministan Isra’ila bayan da jam’iyun adawan kasar, suka dunkule wuri guda suka kafa gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da gwamnatin hadakar.

Netanyahu shi ne Firai Ministan da ya fi dadewa akan wannan mukami, inda ya kwashe shekara 12.

Jam’iyyu takwas ne suka dunkule wuri guda don kafa sabuwar gwamnati.

Wannan gwamnatin hadaka ta kawo karshen rashin tsayayyiyar gwamnati da kasar ta Isra’ila ba ta da ita, abin da ya sa aka yi zabuka har hudu cikin shekara biyu kafin a kai da kafa wannan gwamnatin hadaka.

Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu looks at U.S. Secretary of State Anthony Blinken (not pictured) during a joint news conference in Jerusalem, May 25, 2021.
Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu looks at U.S. Secretary of State Anthony Blinken (not pictured) during a joint news conference in Jerusalem, May 25, 2021.

Sabuwar gwammnatin Bennet mai ra’ayin mazan jiya, wanda dan jam’iyyar Yamina ne, za ta yi wa’adin shekara biyu.

Zai kuma mika wa Yair Lapid, shugaban masu matsakaicin ra’ayi na Yesh Atid, don ya karasa sauran shekara biyu.

Masu shari na hangen baya ga shan kaye da ya yi, Netanyahu na kuma fuskantar tuhume-tuhume kan zargin cin hanci da rashawa.

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG