Mai martaba, Andoma na Doma, Alhaji Aliyu Onawo shi ya jagoranci wannan zaman sulhun da ya tattaro sarakunan Fulani da na Tibi da kungiyar Miyetti Allah na garin Doma.
Tashe-tashen hankulan da ke ta aukuwa bai haifar da komai ba face hasara ga manoman da makiyayan, kuma ana cikin hadarin fadawa cikin yanayin karancin abinci idan har ba a samu maslaha ba, inji shugaban Miyetti Allah reshen Doma, Alhaji Bello Inusa.
“Shawarar da mu Fulanin yankin Doma muka dauka musamman dangane da iyakokinmu shine, za mu amince kowane manomi ya koma gonarsa ya yi aiki ba tare da fargabar wani abu da zai cutar da shi ba. Za mu kuma zauna da sauran ‘yan uwanmu Fulani domin mu gaya musu cewa zaman lafiya ne muke bukatar gani a Najeriya,” inji shugaban Miyetti Allan
Shugaban kuma ya bayyana bukatar zama da sauran sarakunan jihohin Benue da Nassarawa domin su ja kunnen yaransu daga shiga iyakokin juna don kai hare-hare. Sannan za su yi iya kokarinsu wajen bankado masu tada zaune tsaye.
“Duk wani da muka gane cewa na cikin masu kawo tashin hankali suna jawo mana bakin jini, sai mun hada shi da jami’an tsaro,” inji Bello Inusa
Sai dai shugaban kungiyar matasan Tibi a jihar Nassarawa, Peter Ahemba, ya nuna bakin cikinsa cewa duk da zaman sulhun da aka yi, an sake kashe wasu da ke gudun Hijira
“Daman mutanen sun riga sun gudu amma sai suka sake komawa gida domin dauko wadansu abubuwa da suka baro.To da shigarsu ne aka kashe mutane 8 da bindiga. To wannan ya bamu mamaki,” inji Peter Ahemba
Ahemba ya bayyana cewa hakan bai sa sun yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da alkawarinsu na neman zaman a jihar Nasarrawa.
Gwamnan Jihar, Tanko Almakura ya shaida za su ci gaba da kokarin ganin tabbatar da tsaro da kulawa da wadanda suka gujewa rikici a garuruwansu har sai abubuwa sun lafa.
Saurari cikakken rohoton Zainab Babaji
Your browser doesn’t support HTML5