Hukumar lafiya ta duniya ce ta ware wannan mako domin ganganmin fadakar da mutane da sauran masu ruwa da tsaki kan muhimmancin bada rigakafi ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar, da nufin kare su daga cututtuka masu saurin illata su ko hallaka su baki daya.
A can baya dai wannan yunkuri na bada rigakafi ya gamu da turjiya daga jama’a, hakan ya sa gwamnatoci a matakai daban-daban a Najeriya tare da hukumomi da kungiyoyin rajin kiwon lafiyar Jama’a na ciki da wajen kasar suka himmatu domin wayar da kan al’umma.
Dakta Muntaqa Maude, likita ne dake aiki a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya ce rigakafi taimako ne da ake yiwa garkuwar jikin dan Adam, musamman kananan yara ta yadda zai kare su daga cututtuka.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum