Neja: Kotu Ta Ki Amincewa Ta Bada Belin Tsohon Gwamna

Tsohon Gwamnan Neja Dakta Mu'azu Babanhida Aliyu Tare Da Umar Nasko a Kotu

Kotu a Minna ta ‘ki amincewa da bada belin tsohon gwamnan jihar Neja Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, inda za a ci gaba da tsare shi saboda zargin yin almundahana da dukiyar gwamnati lokacin da yake kan mulki a jihar Neja.

Kotun dai ta tura tsahon gwamnan Dakta Mu’azu Babangida Aliyu gidan yari, bisa tuhumar da ake masa na karkatar da sama da Naira Miliyan Dubu Biyar a lokacin da yeke gwamnan jihar Neja.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta garzaya kotu inda ta zargi tsohon gwamnan tare da tsahon kwamishinan sa na ma’aikatar muhalli Alhaji Umar Nasco, da laifin yin sama da fadi da makurdan kudaden gwamnati.

Alkalin kotun mai Shari’a Aliyu Mai Yaki, ya amince da bukatar lauyan hukumar EFCC na ci gaba da adana tsohon gwamnan Babbangida Aliyu da Umar Nasco, domin ci gaba da gudanar da bincike akan laifin da ake zarginsu da aikatawa.

Sai dai kuma lauyan da ke kare tsohon kwamishinan Alhaji Umar Nasco, yace basu ji dadin kin bada belin ba, kasancewar ba shi bane gwamna ba.

An dai share kimanin sa’o’i takwas ana tafka muhawara tsakanin lauyoyi game da tsohon gwamnan ba tare da samun nasara ba. Shugaban jam’iyyar PDP a jihar Neja, Barista Tanko Beji, yayi kira ga sauran ‘yan jam’iyyar da cewa su yi hakuri domin lauyoyi na nan suna aikin ganin an sako da Dakta Mu’azau Babagana Aliyu.

Zaman shari’ar dai ya dauki hankulan jama’a matuka ta re da jibge jami’an tsaro fiye da kima a harabar kotun, yanzu haka dai mai shari’a Aliyu Mai Yaki, ya saka ranar uku ga wata mai kamawa domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Neja: Kotu Ta Ki Amincewa Ta Bada Belin Tsohon Gwamna - 2'57"