Koina inda mutane ke taruwa a fadin jihar ta Kano kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake yi akan wannan badakala da ta kunno kai a masarautar Kano.
Ibrahim Abdullahi yace tarihi ne ke maimaita kansa saboda sarkin yanzu Muhammad Sanusi ll ba mutum mai tsoro ba ne. Ya gaji kakansa sarki Sanusi na daya. Mutum ne mai tsayawa kan gaskiya. Yace kakansa ma an bincikeshi.
Shi kuwa Umar Ibrahim Usman cewa yayi yana goyon bayan gwamnati ta binciki lamarin saboda zarmiya tayi yawa a Najeriya. Yana mai cewa ya kamata a tabbatar da mai gaskiya.
Umar Abdulwahid yace ana hangen masarauta tana da laifi ai gwamnati ma tana da laifi. Yace idan an taba masarauta shi ba zai ji dadi ba saboda an ga sarki na taimakawa jama'a sun soma adawa dashi domin su tsigeshi.
Yace bayin Allah mata da goyo da 'ya'yansu ana taimaka masu suna adawa dashi.
Gwamnatin tarayya da tace zata taimaka masu bata yi ba amma tana son ta binciki mai taimako. Yace su ma suna binciken gwamnati akan taimakon da suka ce zasu yi amma basu yi ba.
Sadiq Galadima yace duk wanda yake da laifi hukuma tana da hurumin ta bincikeshi.
Masu kula da al'amura suna cigaba da fashin baki akan batun. Dr. Musa masanin kimiyar zamantakewa ne kuma yayi sharhi akan harkokin da suka safi mulkin fada.
Yace masarauta tana da wani matsayi akan zukatan al'umma shi ya sa ana ganin sarki uban kowa ne. Ana ganin yana da wani iko na tafiyar da kudaden dake tare dashi ba tare da tilas ya fiti ya yiwa 'ya'yansa bayani ba..Yace kowa ya kamata ya ja kimarsa, ya ja darajarsa.
Masarauta ta ja kimarta ta rufe kofofin da ta bude da suka sa ana kawo mata farmaki. Gwamnati kuma ya kamata ta gane taba masarauta tamkar taba darajar sarkin dake kan karagar mulki ne. Taba masarauta na daidai da taba mutuncin al'umma.
Ranar biyu ga wata mai zuwa ne jami'an masarautar zasu amsa sammacin da hukumar EFCC ta aika masu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani..
Facebook Forum