Sakataren gudanarwa na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jihar Adamawa Malam Salihu Ya’u ya ba da tabbacin haka a taron masu ruwa da tsaki na shugabannin jam’iyun siyasa, jami’an tsaro, kungiyoyin sa ido kan harkar zabe da kafofin yada labarai don nazarin shirye-shiryenta na soma aikin sabunta katunan zabe da rajistar sabbin wasu.
Wasu daga cikin batuttuwan da mahalarta taron suka nuna damuwa a kai, sune na ‘yan gudun hijira da Boko Haram ta raba da muhallinsu saboda sharudan da hukumar zaben ta gindaya kamin ta sabunta masu katin zabe da kuma kutare da a zaben 2015 da ya gabata ba su sami damar kada kuri’a ba sakamakon rashin tanadi domin su.
Bakin shugaban jam’iyar adawa ta PDP ta jihar Adamawa Barr, Abdulrahaman Bobboi da na sakataren tsare-tsare na jam’iyar APC Alhaji Ahmed Lawan ya zo daya inda suka nemi hukumar zabe ta kasa ta sassauta sharudan da ta gindayawa masu neman sabunta katinsu da kuma kutare don su sami dama kamar kowane dan kasa a zabubbuka masu zuwa.
Ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke kananan hukumomi ashirin da daya na jihar Adamawa na gudanar da tarurrukan masu ruwa da tsaki kan harkar soma rajistar masu zabe kana kuma ta kaddamar da gangamin fadakar da al’uma muhimmancin sabunta katin zabe da yi wa masu kada kuri’a rajista ta kafofin yada labarai.
Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum