Kamfanin jiragen saman Max Air ya dakatar da zirga-zirgarsa tsawon watanni 3 biyo bayan hatsarin da ya afku da daya daga cikin jiragensa masu safara a cikin najeriya a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, da ke Kano.
Jami'i mai magana da yawun hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Najeriya (NCAA), Michael Achimugu, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a yau Laraba, sa'o'i bayan afkuwar hatsarin na daren Talata a filin saukar jiragen saman Kano.
Yayin sauka a filin saukar jiragen saman da misalin karfe 10 da mintuna 51 na dare, jirgin ya gamu da matsalar lalacewar kafar gaba tare da fashewar taya yayin da ya sauka a kan titin filin saukar jiragen abin da ya jefa fasinjoji cikin firgici.
Sai dai, ma'aikatan jirgin 6 da fasinjoji 53 ba su samu wasu raunuka ba sakamakon hatsarin.
A cewar hukumar dake kula da filayen jiragen saman Najeriya (FAAN), tuni aka janye tarkacen jirgin daga kan titin kuma an ci gaba da zirga-zirgar a filin saukar jiragen saman.
An gudanar da binciken tantance amincin jiragen saman kamfanin Max Air bayan da tayar daya daga cikin jiragensa dake safarar cikin gida ta fashe yayin da yake kokarin sauka a filin saukar jiragen saman Malam Aminu Kano a daren jiya Talata.
Wata majiya ta shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar aikin binciken ya fara nan take bayan afkuwar hatsarin daya afku da misalin karfe 10.57 na daren jiya Talata sa’ilin da jirgin daya taso daga tashar jiragen sama ta Murtala Muhammad dake Legas ya sauka a Kano.
Jirgin saman ya gamu da matsalar fashewar taya, al’amarin da ya haddasa tsoro da fargaba a zukatan fasinjoji sai dai an yi nasarar kwashe dukkanin mutanen da ke cikinsa ba tare da wasu raunukan ba.
Rahotanni sun bayyana cewa me yiyuwa tayar gaban jirgin ce ta daina aiki, al’amarin da ya sabbaba hatsarin.