Kungiyar tsaron NATO tana binciken ikirarin da Taliban ta yi cewar ita ce ta harbo wani jirgin helkwafta na sojojin Amurka a tsakiyar Afghanistan har ta kashe mutane 38, cikinsu har da zaratan sojojin Amurka.
An ci gaba da gwabza fada yau lahadi a lardin Wardak inda wannan helkwafta samfurin Chinook CH-47 na sufurin dakaru ya fadi daren jumma’a. Sojojin Amurka 30, cikinsu har da ‘yan rundunar zaratan nan da ake kira Navy Seals, sun mutu tare da sojojin kundumbala 7 na Afghanistan da wani tafinta guda daya.
Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa ita ce ta harbo jirgin. Dakarun gwamnatin Afghanistan a wurin sun ce helkwaftar ta fado ne a bayan da aka harbe ta da roka. Wannan lamarin ya faru a bayan wani farmakin da Amurka ta jagoranci kaiwa a kan wani gida na ‘yan Taliban da aka gano inda aka kashe tsagera 8.
Wannan ita ce hasarar rayuka mafi muni a hari guda da sojojin kawance suka fuskanta tun lokacin da aka fara yakin Afghanistan kusan shekaru goma da suka shige.
A wasu jawabai dabam-dabam, sakataren tsaron Amurka Leon Panetta da sakatare janar na kungiyar NATO Anders Fogh Rasmussen sun ce sojojin kawance zasu ci gaba da gudanar da ayyukansu a Afghanistan. Kungiyar NATO ta fara mayar da hakkin ayyukan tsaro ga sojojin Afghanistan a wasu sassan kasar, a wani bangare na shirin janye dukkan sojojin kai farmaki na NATO nan da karshen shekarar 2014.
A wani sabon tashin hankalin dabam kuma, NATO ta ce an kashe mata sojoji 4 yau lahadi a wasu hare-hare guda biyu na ‘yan tawaye a kudancin Afghanistan da kuma gabashin kasar.