Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Mutane Da Suka Halaka A harin Kunar Bakin Wake A Afghanistan Ya Karu

Wani mutum da ya jikkata daga wani hari da aka kia a lardin Kunduz.
Wani mutum da ya jikkata daga wani hari da aka kia a lardin Kunduz.

Jami’an Afghanistan sun ce adadin wadanda suka halaka sakamakon harin kunar baki wake da aka kai kan wani asibiti ya kai 38, kuma galibin wadanda harin ya rutsa dasu mata ne da yara.

Jami’an Afghanistan sun ce adadin wadanda suka halaka sakamakon harin kunar baki wake da aka kai kan wani asibiti ya kai 38, kuma galibin wadanda harin ya rutsa dasu mata ne da yara.

Yau lahadi ce hukumomin kasar suka bada sabon adadin, su kara da cewa akalla mutane 50 ne harin da aka kai gabahsin kasar suka jikkata.

Jiya Asabar ce aka kai harin a gundumar Azra dake cikin lardin Logar dake dab da kan iyakar kasar da Pakistan.

Hukumomin Afghanistan suka ce wata motar shakatawa ce da aka dankarawa nakiya ta aukawa asibitin ta rusa ginin baki daya, mutane da dama ne baraguzan ginin suka danne.

Kungiyar Taliban ta musanta ita take da alhakin kai harin,duk da haka abu ne sannane kungiyar tana da karfi kuma tana kai hare hare a yankin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG