Nasarar Kungiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Tsakanin Mabiya Addinai A Najeriya

Daya daga cikin wuraren da yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a N'Djamena, Chadi

Sakamakon nasarorin da kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addnin Krista da Musulmai ta kasa da kasa ta cimma bayan rarrabuwar kawuna da rikicin Boko Haram ya haddasa a Arewa maso Gabashin Najeriya, kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afirka ta baiwa wannan kungiya kujera a kwamitin sulhun ta.

Kimanin ‘yan kungiyar Boko Haram dubu daya suka tuba kuma suka mika wuya a kasar chadi makwabciyar Najeriya da yanzu haka hukumomin ke dubu yiwuwar maida su cikin sauran jama’a.

Shugaban wanzar da zaman lafiya sakanin mabiya addinin Krista da Musulmai na kasa da kasa a Najeriya, Imam Dokta Mohammed Ashafa, ya bayyana haka biyo bayan ziyarar shiga tsakani don dinke barakar da aka samu sakanin al’umomin Arewaci da Kudancin da suka kai kasar.

Yace akwai bukatar kasar Najeriya su yi koyi da nasarorin da Chadi suka cimma wajen hadin kan al’umomin kasar inda suka zama tsintsiya madaurin ki daya, baya rarrabuwar kawuna biyo bayan juyin mulkin kasar.

Shima daraktan kungiyar Fasto Dokta James Morgan Wuye, yace sun kai ziyara kasar Chadi ne don koya musu yadda zasu sarrafa takaddama da kuma gano ta, a duk lokacin da ta kunno kai kafin ta hayayyafa ba tare da hukuma ta tsoma baki ba.

Yace babbar nasarar wanna ziyara ta su itace ta samun kujera a kwamitin sulhu na kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika.

Domin Karin Bayani saurari rahotan Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarar Kungiyar Wanzar Da Zaman Lafiya Tsakanin Mabiya Addinai A Najeriya - 3'03"