Gwamna Lawal ya sake jaddada aniyar ganin cewa nan da dan lokaci kadan za a kama ko hallaka jagoran ‘yan ta’addar.
Lokacin da aka tambayeshi game da yiyuwar dakatar da ayyukan kasurgumin dan bindigar a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels me suna “Politics Today” a jiya Litinin, gwamnan yace “lokaci kawai ake jira”.
“Da irin wannan tsari da muke da shi a kasa, na hadin gwiwa tsakaninmu (gwamnatin jiha) da ta tarayya da hukumomin tsaro, ina baku tabbacin cewar, lokaci kawai ake jira; amma za a hallaka Turji nan da lokaci kadan.”
Kalaman gwamnan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da dakarun sojin Najeriya suka samu gagarumar nasara akan ‘yan bindiga, inda suka hallaka dan bindigan da aka jima ana nema Halilu Sububu, wanda ya addabi al’ummar jihohin Zamfara da Sokoto da sauran sassan arewa maso yamma.
Ku Duba Wannan Ma Sojojin Najeriya Sun Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Halilu Sububu Ku Duba Wannan Ma Kwanakin Bello Turji Da Sauran ‘Yan Bindiga Sun Kusa Karewa – Janar Chris MusaA makon da ya gabata an hallaka Halilu Sububu da fiye da ‘yan bindiga 30.