Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanakin Bello Turji Da Sauran ‘Yan Bindiga Sun Kusa Karewa – Janar Chris Musa


Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa

Ya kuma bayyana kisan kasurgumin dan ta’addar nan Halilu Sububu da ya addabi jihar Zamfara a matsayin wata nasara da dakarun suka samu.

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewar lokaci ya kusa kurewa jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda kasancewar dakarun sojin kasar sun himmatu wajen kawo karshen rashin tsaro a Zamfara da ma yankin arewa maso yamma baki daya.

Babban hafsan tsaron ya bayyana hakan ne a jihar Zamfara, dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya, a wata kebabbiyar da Muryar Amurka.

Ya kuma tabbatar da hallaka kasurgumin dan ta’addar nan Halilu Sububu da ya addabi jihar Zamfara a matsayin wata nasara da dakarun suka samu.

Kasurgumin dan ta’addar ya gamu da ajalinsa ne a Kwaren Kirya, wani kauye a karamar hukumar Maru.

A saurari cikakken hirar Janar Musa da Muryar Amurka:

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Tabbatar Da Hallaka Halilu Sububu
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG