Nama Zata Yi Tsada a Legas, Saboda Rufe Babbar Mayanka Dake Birnin

Yara suke wasa da shanun da ake amfani dasu wajen yin huda.

Gwamnatin jihar Legas ta rufe babbar mayankan dabbobi dake birnin na Ikko.

Gwamnatin jihar tace ta dauki wannan matakin ne saboda rashin tsabta da mayankan yake fama dashi. Gwamnatin ta bakin jami'anta suka ce ya zama tilas ta dauki wannan mataki ne saboda daya daga cikin hanyoyi da cutar Ebola take ke yaduwa, ko dalilai da suke haddasa cutar rashin tsabta yana daga cikinsu. Shine yasa gwamnati ta dukufa wajen ganin ta hana cutar samun gindin zama a jihar.

Wakilin Sashen Hausa ladan Ibrahim Ayawa, wanda ya ziyarci mayankan yace ko shakka babu wurin yana buktar a tsafta.

Ya zanta mahautan da suke aiki a wurin ga irin bayani da suka yi masa.

Your browser doesn’t support HTML5

An kulle mayankan jihar legas.