Har yanzu jama'a da dama musamman ma masu shigi da fici a kasashen Nijer da Najeriya na ci gaba da bayyana fargabar su kan cutar Ebola da ke barazana a kasashen Yammacin Afrika.
Ko da yake gwamnatocin kasashen biyu na ci gaba da kara kaimin daukar matakan kariya a kan iyakoki ta hanyar gwada masu shiga da fita kasashen biyu, kamar yadda za ku ji a cikin rahoton nan da Wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko.
Wakilin na Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou yayi tattaki ne zuwa Birnin Konnin tare da tawagar shugaban sashen Hausa na muryar Amurka Leo Keyen wanda ke ziyarar aiki a Nijer yanzu haka, tawagar ta kai ziyara Birnin Konni dake kudu maso yammacin kasar Nijer wanda kuma yayi iyaka da Sokoto ta bangaren Najeriya.
Tawagar shugaban Sashen Hausa Leo Keyen ta kai ziyara Birnin Konni ne domin ta ga irin kokarin da hukumomin Najeriya da Nijer ke yi a kan iyakokin su domin yaki ta cutar Ebola.